Gwamnonin PDP Sun Gana Da Zababben Shugaban Ƙasa A Abuja

Alfijr ta rawaito Gwamnonin PDP sun ziyarci Tinubu a Abuja, yayin ganawar sun yi kira ga yan Najeriya da su marawa zababben shugaban kasa baya musamman yan jam’iyyar PDP, sun ziyarci zababben shugaban kasa Bola Tinubu a gidan tsaro. Abuja, ranar Juma’a.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, sun gana da shugaban kasa mai jiran gado.

Gwamnonin biyu dai na daga cikin gwamnonin G-5 na jam’iyyar PDP da suka ki yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da Tinubu ya lashe ranar 25 ga watan Fabrairu aiki.

Sun dage kan cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus a yayin da ake tunkarar babban zabe.

Wata majiya a sansanin Tinubu ta bayyana a daren Juma’a cewa gwamnonin biyu sun gana da Tinubu a Abuja, amma sun dage cewa ganawar ba ta da wata manufa ta siyasa.

Ya ce, “Zababben shugaban kasa, Gwamna Seyi Makinde, Asiwaju Bola Tinubu da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike sun hadu a Abuja yau.

“Sun ce sun zo ne domin mubaya’a ga zababben shugaban kasa; cewa zabe ya kare kuma lokaci ya yi da za a fuskanci mulki, kuma za su marawa Tinubu baya tare da ba su hadin kai don samun nasara da kuma mayar da arzikin kasa.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *