Jami’an Yan Sanda Sun Kama Bindigogin Kirar AK-47 A Kano

Alfijr ta rawaito ƴan sanda sun kama bindigogi kirar AK-47 guda hudu a kokarin yin fasakwaurinsu zuwa Kano.

A ranar Juma’a ne ’yan sanda yayin sintiri a Kwanar Garko da ke kan hanyar Bauchi zuwa Kano suka gano bindigogin a  cikin wata motar bas kirar Hiace.

Masu motar na hango ’yan sanda, sai motar ta fara kokarin juyawa, inda daya daga cikin mutanen motar ya fito ya jefar da kunshin wani abu a cikin buhu, suka ja motar suka tsere.

Daga baya da ’yans sanda suka duba sai suka gano bindigogi kirar AK-47 guda hudu a ciki.

Da yake sanar da hakan, kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce rundunarsu tana ci gaba da bincike domin kamo mutanen da suka tsere.

A nasa bangaren, Mukkaddashin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, DCP Mu’azu U. Mohammed, ya jinjina wa mutanen jihar kan hadin kan da suke ba wa rundunar.

Ya kuma bukace su da su kai rahoton duk wani wanda ba su aminta da motsinsa ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *