Hedikwatar Tsaro Ta Najeriya Ta Bayyana Sunayen Yan Ta’adda 97 Da Take Nema Ruwa a Jallo

ALFIJIR 1

A ƙalla ‘yan bindiga, ɓarayin daji da tsageru 97 ne Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja ya bayyana a matsayin waɗanda yake nema ruwa a jallo.

Alfijir labarai ta rawaito Ofishin ya ce waɗanda yake neman suna da hannu wajen aikata manyan laifuka da tada zaune tsaye a sassan ƙasa.

Har wa yau, waɗanda lamarin ya shafa ya haɗa da shugaban wani ɓangare na tsagerun IPOB, wato Simon Ekpa.

Mai magana da yawun rundunar soji, Manjo-Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana sunaye da hotun waɗanda rundunar ke farautarsu.

Sunayen da aka fitar ya haɗa da na wasu mutum 43 dag yankin Arewa maso Yamma kamar su:

Alhaji Shingi; Malindi Yakubu; Boka; Dogo Gide; Halilu Sububu; Ado Aliero ; Bello Turji; Dan Bokkolo; Labi Yadi ; Nagala; Saidu Idris; Kachalla Rugga da kuma Sani Gurgu da sauransu.

Sai kuma shiyyar Arewa maso Gabad mai fama da mayaƙan Boko Haram da ISIS inda aka ayyana mutum 33 da suka haɗa da:

Abu Zaida; Modu Sulum; Baba Data; Ahmad; Sani Teacher; Baa Sadiq; Abdul Saad; Kaka Abi; Mohammad Khalifa; Umar Tella; Abu Mutahid; Mallam Mohammad; Mallam Tahiru Baga; Uzaiya and Ali Ngule da sauransu.

A yankin Arewa ta Tsakiya, mutum 21 ne aka ayyana da suka haɗa da Simon Ekpa; Chika Edoziem; Egede; Zuma; ThankGod; Gentle; Flavour; Mathew; David Ndubuisi; High Chief Williams Agbor; Ebuka Nwaka; Friday Ojimka; Obiemesi Chukwudi aka Dan Chuk; David Ezekwem Chidiebube da kuma Amobi Chinonso Okafor aka Temple da sauransu

FB IMG 1711195193351
Yan ta adda

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *