Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kano sun kama wani direban babbar mota da laifin aika hotunan batsa ga wata matar aure a cikin birnin Kano.
Alfijir labarai ta rawaito wanda ake zargin Sani Muhammad mazaunin unguwar Naibawa ne a cikin birnin, an gano shi tare da kama shi biyo bayan korafin da aka yi a Hukumar Hisbah.
An tattaro cewa uwar gidan ta gargadi Mista Sani da ya daina aika kayan batsa amma ya ci gaba da yin biris da gargadin da ta yi.
Bayan ta shigar da kara ne jami’an Hisbah suka kai wanda ake zargin zuwa wani wuri, inda aka kama shi.
A wata hira da ya yi da wakilinmu, Mista Sani ya amince da aikata laifin, inda ya ce wannan ne karon farko.
“An kama ni da aika hotuan batsa ga wata matar aure. Amma shi ne karo na farko. Ban taba yin haka ba a baya,” inji shi.
Sai dai Mista Sani mai shekaru 26, ya roki Hukumar Hisbah da ta yi masa sassauci, inda ya yi alkawarin ba zai sake maimaita laifin ba a nan gaba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk