Hisbah Ta Kama Mutane 14 Bisa Zargin Karuwanci Da Sayar Da Miyagun Ƙwayoyi

Screenshot 20240312 221118 com.facebook.katana edit 2751549873537

Rundunar Hisbah ta jihar Yobe ta kama wasu mutane 14 da ake zargi da laifin karuwanci da safarar miyagun kwayoyi.

Alfijir labarai ta rawaito Yusuf Yusuf, babban sakataren ma’aikatar harkokin addini ta jihar ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a yau Talata a Damaturu.

Yusuf ya ce wadanda ake zargin sun hada da mata tara da maza biyar, ya kara da cewa an kama su ne bayan wani samame da aka kai a Damaturu da suka hada da Gidan Ajayi, Zango, Bus Stop, da sauransu.

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin za a mika su ga jami’an tsaro domin gurfanar da su gaban kuliya, yayin da sauran kuma za a yi musu nasiha kan gyaran halaye.

“Wasu kuma za a yi musu nasiha daga malaman addinin Musulunci, da fatan gyarawa,” inji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *