Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane 24 a wani samame da suka kai a wani gidan biki da aka gudanar a wata babbar unguwa a cikin birnin.
Alfijir labarai ta rawaito an kai samame ne a ranar Alhamis a wani katafaren gida da ke Alu Avenue, a karamar hukumar Nasarawa a jihar.
Jami’an Hisbah sun shaida wa wakilinmu cewa, farmakin ya biyo bayan korafe-korafen da mazauna unguwar suka yi cewa matasa maza da mata kan shirya liyafa a gidan, inda ake zarginsu da aikata laifukan da ba su dace ba.
A yayin samamen jami’an Hisbah sun cafke mata 15 da maza 9, wadanda adadinsu ya kai 24.
An tattaro cewa galibin ‘yan matan sun halarci bukukuwan ne bayan sun yaudari iyayensu cewa sun tafi makaranta.
Daya daga cikin matan da ta bayyana kanta a matsayin Fatima ta yi ikirarin cewa an kama ta ne bayan ta karbi abinci a gidan.
“Yan uwana mata guda biyu sun jira a adaidaita sahu suka aiko ni in dauko abinci a gidan. Amma da na fito sai Hisbah ta kama ni.
Fatima ta ce bayan sun gama makaranta ne suka yanke shawarar zuwa gidan.
Wata baiwar Allah ta ce cikin kuka ta raka kawarta mai suna Madina zuwa wurin walima aka kama ta.
“Kawata Madina ce ta gayyace ni bikin, ta ce a gidan abinci 10 to 10 ne. Amma da muka shiga gidan cin abinci, saurayinta ya kira ta ya ce an yi taron ne a wani gida mai makwabtaka da Wajen.
“Bayan mun shiga ne jami’an Hisbah suka bude kofar suka kama mu. Na gaya wa iyayena cewa zan je makaranta amma na je biki idan mun gama lectures,”
A hirarsa da Daily News 24, Mataimakin Kwamandan Hukumar (DCG) Sheikh Muhajid Aminuddeen, ya ce abin takaici ne yadda masu laifin suka yanke shawarar gudanar da haramtattun bukukuwa a wani wuri kusa da masallaci.
“Makwabta sun yi mana korafin cewa maza da mata suke haduwa tare da yin abubuwan da ba su dace ba suna faruwa a gidan tsawon shekaru. Don haka muka yanke shawarar gudanar da aiki kuma muka yi nasarar cafke wadanda suka aikata laifin,” inji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V