Hukumar DSS Ta Ce Ta Gano Manufar Masu Son Yin Zanga-Zanga A Nigeria

IMG 20231110 230813

Hukumar ta DSS ta ce tuni ta riga ta gano waɗanda suka kitsa ta da masu goyon bayan zanga-zangar, inda suka gargaɗe su da su sanya kishin ƙasa su dakatar da shirin zanga-zangar.

Alfijir labarai ta ruwaito gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dakta Peter Afunanya ya aike wa manema labarai.

Sanarwar ta ce hukumar ta DSS ta gano cewa wasu ɓatagari na shirin karkatar da akalar zanga-zanagr da manufar tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Dakta Afunanya ya kuma yi zargin cewa burin masu kitsa zanga-zangar shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya.

“Masu kitsa zanga-zangar na son yin amfani da haddasa hatsaniya domin shafa wa gwamnatin tarayya da na jihohi kashin kaji da ɓata musu suna domin haɗa su da talakawa. Burinsu shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya.” In ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ta duk da cewa ta gano masu kitsa zanga-zangar da masu ba su kuɗaɗe amma hukumar tana bin hanyoyin da doka ta tanada waɗanda ba na amfani da ƙarfi ba domin daƙile zanga-zangar.

Daga ƙarshe hukumar ta nemi iyaye da shugabannin gargajiya da malamai su ja hankalin mabiya da ƴaƴansu da ɗalibai da su guji shiga wannan zanga-zangar.

Sai dai kuma duk da haka hukumar ta ce za ta yi aiki tare da sauran jami’an tsaron ƙasar wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *