Hukumar DSS Ta Gayyaci Tsohon Ministan Sufuri Hadi Sirika

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kan takaddamar jirgin saman Nigeria Air.

Alfijir Labarai ta rawaito tsohon ministan Sirika ya isa hedikwatar DSS da ke Abuja domin amsa tambayoyi game da cece-kucen da aka yi na kaddamar da jirgin.

A

Sirika ya isa hedikwatar da misalin karfe 3 na yammacin ranar Alhamis a cikin wata mota kirar Range Rover Sport Utility Vehicle (SUV).

Idan za a tuna cewa a watan Mayu gwamnatin Muhammadu Buhari ta kaddamar da wani jirgin Boeing 737-800 na kamfanin jiragen saman Habasha a matsayin jirgin saman Nigeria Air.

Bayan kaddamar da jirgin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Captain Dapo Olumide, ya bayyana cewa jirgin ya haura shekaru 10, kuma mallakin kamfanin jiragen saman kasar Habasha ne.

Lamarin ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin β€˜yan Nijeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *