Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya ta ci tarar Kano Pillars

📸 kano Pillars

Hukumar kula da gasar firimiya ta Nigeria a ranar Litinin ta ci tarar Kano Pillars kuɗi har Naira miliyan ɗaya, sakamakon kutsen da magoya bayantu suka yi a filin wasa, a wasan da suka fafata da Rivers United.

Alfijir Labarai ta rawaito an tabbatar da cewa magoya bayan ƙungiyar Kano Pillars sun ketara shingen filin wasa domin murnar cin ƙwallon da suka yi a minti na 92 ​​a karawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha.

Bayan nazarin rahotanni daga jami’an wasan, hukumar kula da gasar Firimiya ta Najeriya, NPFL ta tuhumi kulob din da laifin karya doka mai lamba B13.18. Ta hukumar

Don haka an umurci kulob din da ya biya tarar cikin kwana 14, kuma ya ja kunne kan hakan, wanda gaza yin hakan zai zamo tamkar ci gaba da saɓa wa dokokin hukumar ta NPFL.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *