Alfijr ta rawaito hukumar kwastam a Najeriya ta ce ta kama fatar dabbar pangolin da tabar wiwi da wasu ƙwayoyi da suka kai darajar naira biliyan ɗaya.
Dakarun yaƙi da safarar kayayyaki na hukumar ne suka kama 376.4kg na fatar pangloin ɗin, da ƙunshin wiwi 103, da buhun shinkafa ‘yar gwamnati 1,000, da buhuhunan kayan gwanjo 58, da jarakunan man fetur 85.
Fatar dabbar pangolin na cikin abubuwan da aka fi yin safararsu a fain duniya, wadda ake amfani da ita wajen sana’anta abubuwa da yawa.
Mataimakin Kwantirola Sanni Yusuf ya ce sun ƙwace fatar pangolin ɗin a wata kasuwa da ke Ikeja a Legas.
An ɓoye tabar wiwin cikin abubuwa daban-daban ƙunshe a cikin wata mota ƙirar Toyota Camry, in ji shi.
Ya ƙara da cewa tun bayan ƙace kayan, hukumarsa ta yi nasarar tattara kuɗin shiga da suka kai naira miliyan 537.
BBC Hausa
[07/12, 11:35 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇