An Ceto Shugaban Jam’iyyar APC Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

Alfijr ta rawaito rundunar ƴan Sandan jahar Kogi sun ceto Shugaban Jam’iyyar APC daga hannun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, an kuma kama wasu ‘yan bindiga biyu yayin rangadin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO) SP William Aya wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce wadanda ake zargin suna da hannu wajen yin garkuwa da shugaban jam’iyyar APC daga Kogi ta Gabas, Yahaya Shagari.

Aya ya ce, “Jami’an tsaro na hadin gwiwa karkashin jagorancin kwamandan yankin, Idah ACP Alexander Asagade, sun kai farmaki maboyar ‘yan bindigar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a cikin daji, bayan da suka ga jami’an, sai ‘yan bindigar suka tare su fara harbe harbe, har aka sami nasara a kan su.

Daya daga cikin wadanda ake zargin, PPRO ya ce, daga baya an kashe shi, an kuma kama wasu biyu yayin da aka ceto wanda aka yi garkuwar ba tare da wani rauni ba.

“An yi nasarar gudanar da aikin ne biyo bayan sahihan bayanai game da maboyar wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a cikin daji”.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kogi, CP Akeem Yusuf ya yabawa kwamandan yankin da jami’an tsaro na hadin gwiwa da suka yi a lokacin aikin.

Ya bukace su da su ci gaba da kai hare-hare a kan masu aikata laifuka a yankin da suke da alhakin.

Aya ya tabbatar wa jama’a matakin da rundunar ta dauka na yin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro a jihar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

[07/12, 11:35 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *