Hukumar NDLEA ta Kwace Magungunnan Biliyon 60. N60bn A cikin Watanni Biyu – Buba Marwa

 Hukumar NDLEA ta Kwace Magungunnan N60bn A cikin Watanni Biyu 

Best Seller Channel 

 Best Seller Channel 

Hukumar Yaki da Sha fataucin miyagun kwayoyi  ta Kasa ta ce, a cikin watanni biyun da suka gabata ta kwace wasu magungunan da suka kai Naira biliyan 60.

 Janar Muhammed Buba Marwa (rtd) ne ya bayyana haka a taro na uku na kungiyar Galaxy Clique da ke garin Offa a karamar hukumar Offa ta jihar Kwara. 

Leadership ta rawaito  Kayode Babayeju, wakilin kwamandan NDLEA na jihar Kwara, a wajen taron mai taken “Hard Drug Abuse and Insecurity: A Siamese Twins”, ya bayyana cewa kashi 99 cikin 100 na laifukan da ake tafkawa a kasar nan suna cikin ta’ammali da miyagun kwayoyi. 

Best Seller Channel 

Marwa ya ce masu aikata laifukan da ke addabar al’ummomi daban-daban suna zaune a tsakanin jama’a kuma ya bukaci jama’a da kada su kare su.

 Ya kara da cewa yawan amfani da muggan kwayoyi yana haifar da cin zarafi, inda ya bayyana tabar wiwi a matsayin maganin da aka fi amfani da shi a kasar.

 Shugaban NDLEA ya ja kunnen ‘yan kasar kan amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta tare da tabbatar da cewa hakan na iya kawo illa ga rayuwar su. 

“Tare da kamfen na ci gaba da gudana a cikin ƙasa baki ɗaya, yana yiwuwa a raba shan miyagun ƙwayoyi da rashin tsaro, duk da imanin cewa su tagwaye ne. 

Best Seller Channel 

Muna bukatar mu yi magana da matasanmu don rage shan muggan kwayoyi domin tayar da kayar baya, ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami na da alaka da shaye-shayen miyagun kwayoyi,” in ji Marwa.

Slide Up
x