Hukumar NJC zata hukunta wadanda suka kawo rudanin kan hukuncin kotun daukaka kara a gwamnan Kano 

FB IMG 1701255547603

 Hukumar dake kula da shari’a ta kasa (NJC) ta sha alwashin hukunta jami’an shari’a da suke da alhaki wajen haifar da rudani game da  hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan rikicin zaben gwamnan Kano.

Alfijir labarai ta rawaito hukumar ta bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da jami’an NJC suka kai hedkwatar kamfanin Media Trust Limited da ke Abuja ranar Talata, kamar yadda Daily trust ta ruwaito.

Idan zaku tuna cewar, Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar 17 ga Nuwamba, 2023 ta soke zaben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da bayyana abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna na jam’iyyar adawa ta APC nasara a matsayin gwamnan jihar kano.

 Amma a cikin takardar kundin bayanan hukuncin kotun da aka fitar kwanaki hudu bayan yanke hukuncin, kotun daukaka kara a rubuce ta canja bayaninta tare da bayyana Abba Kabiru Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben a karshen takardar.

 Sai dai jami’an hukumar Shari’ar sun ce sun samu koke da yawa kan lamarin inda suka yi alkawarin yin nazari tare da ɗaukar matakin da ya dake ga wadanda aka samu da laifin haddasa rudani kan hukuncin na kano.

 “Ba za a yi gaggawar yarda da koke-koken ba, sai an tantance korafe-korafe da farko, wadanda za su duba, sai su aika zuwa zauren majalisa, sai majalisar ta duba ta kuma kafa kwamiti. Za a kirawo alkali da masu shigar da koken domin bin diddigi,” shugaban tawagar ya shaida wa jaridar.

 Jami’in na NJC ya ce hukumar da ke kula da shari’a za ta binciki cece-kucen da ake yi duk da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hada da CTC da suka saba wa hukuncin kotun daukaka kara a matsayin batun daukaka kara a kotun koli.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *