Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na binciken zargin almundahana a shirin tura ɗalibai karatu ƙasar waje a kano

FB IMG 1719920231770

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta fara bincike kan zargin almundahana a tallafin karatu na ƙasashen waje.

Alfijir labarai ta rawaito hukumar tana yi wa manyan jami’an ma’aikatar ilimi mai zurfi na jihar tambayoyi game da batun dalibai 1,001 da ake ikirarin suna karatu a Indiya da Uganda.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin dalibai 1,001 masu neman digiri na biyu don yin karatu a Indiya da Uganda.

Shirin yana cikin tsare-tsaren tallafin karatu na kasashen waje wanda gwamna Abba Yusuf ya ƙaddamar.

Kwanan nan, Yusuf ya shirya liyafar bankwana ga rukunin farko na dalibai 550 da suka ci gajiyar tallafin a gidan gwamnati, inda ya jinjina wa tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso kan kirkiro shirin.

Sai dai NAN ya samu labarin cewa ɗalibai 418 ne kawai aka tura zuwa kasashen waje don karatu, wanda ya haifar da tambayoyi kan inda sauran ɗaliban suke.

Da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na hukumar, Kabiru A. Kabiru, ya tabbatar da rahoton, yana mai cewa an yi wa manyan jami’ai biyu tambayoyi kan zargin almundahana ta tallafin karatu.

Ya ce ana gudanar da bincike don gano waɗanda ke da alhakin zargin damfarar da kuma hukunta su.

“Binciken farko ya gano ayyukan almundahana a ofishin ma’aikatar ilimi mai zurfi kan daliban da aka tura don neman digiri na biyu a Indiya da Uganda.

“Mun buɗe bincike don gano gaskiyar lamarin. Duk wanda aka samu da hannu a ciki, za a gurfanar da shi, ba tare da la’akari da matsayin sa ba,” inji Kabiru

(NAN)

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *