Dr Adamu Muhammad Wakil magatakardar Jami’ar Iheris dake kasar Togo yayi wannan martani dangane da kuɗin goro da Ministan Ilimin Najeriya ya yiwa jami’o’in kasashen Benin da Togo.
Alfijir Labarai ta rawaito idan baku manta ba wani dan Jaridar Daily Naigerian mai suna Umar ya bayyana rahoto dake nuna yadda wata jami’a a kasar Benin ke sayar da takardar jabu na shaidar kammala digiri.
Lamarin da ya sa gwamnatin Najeriya ta ce ta rushe karatun da Jami’o’in su kayi tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu, wanda hakan bai yiwa da yawa daga cikin shugabannin jami’o’in dama wasu Yan Najeriya dadi ba.
A tattaunawar sa da manema labarai ciki har da Wakilin gidan Talabijin na ATP Hausa, Dr. Adamu Wakil wanda shine magatakardar Jami’ar ta Iheris ya nuna rashin kwarewa da rashin zurfafa bincike yadda ya kamata daga bangaren gwamnati, ko Kuma kokarin cimma wata manufa ta kashin Kai a matsayin abunda ya haifar da daukan wannan mataki.
A cewar Wakil rahoto irin wannan tsananta bincike ya kamata a yi domin tsamo mai laifi a hukunta shi ba wai ayi kuɗin goro ga wadanda basu ji ba, basu gani ba, ya Kara da cewa yin kuɗin goro tamkar wani shiri ne na kawo koma bayan ga mutane masu ƙoƙarin ganin cigaban harkar ilimi a fadin duniya Baki daya.
Magatakardar ya kara da cewa, ” sanin kowa ne Jami’ar Iheris ta samu lamban yabo akan ingancin Ilimi da nagarta, wanda a halin yanzu akwai dalibanta suna aiki a sassa daban-daban na duniya, dama gida Najeriya da suka hada da hukumomin tsaro, farnin tattalin arziki da sauran muhimman wurare saboda ingancin ilimin da suka samu daga makarantun.
Kazalika, Dr. Wakil ya ce zasu dauki matakin shara ‘a bisa wannan danyen aiki da Ministan Ilimin Najeriya ya zartar domin kuwa tun kafin su fara daukan Dalibai daga Najeriya sai da suka tabbatar sun cika dukkanin ka’idojin da doka ta shimfida, inda hatta ma’aikatar ilimin Najeriya ta basu takardar da ta tabbatar cewa jami’ar ta Iheris ta cika duk wata ka’ida da doka ta tanadar tsakaninta da gwamnatin Najeriya.
Ya bukaci daliban da suka kammala Karatu a Makarantar da ma wadan da ke Karatu a halin yanzu da su sha kuriminsu domin suna yin dukkanin Mai yiwuwa wajen dakile duk wani yunkuri na yin batanci, ko barazana a garesu.
KBC Hausa
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj