Ibtila’i! Dan majalisar dokokin jihar Kano ya rasu

Screenshot 20240407 185420 Chrome

Dan majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Halilu Ibrahim Kundila ya rasu.

Kundila, wanda shi ne dan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Shanono/Bagwai, ya rasu a jiya Asabar da daddare yana da shekaru 59 a duniya.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai a Kano cewa dan majalisar, wanda ya raba kayan tallafin azumi ga al’ummar mazabarsa a makon jiya ya rasu ne a gidansa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni aka yi jana’izar marigayin , wanda dan jam’iyyar APC ne da safiyar yau Lahadi a Kundila da ke karamar hukumar Shanono ta jihar Kano.

Daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar akwai dan majalisar wakilai mai wakiltar Shanono/Bagwai a zauren majalisar tarayya Hon. Yusuf Ahmad Badau.

Marigayin ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 17.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *