Daga Aisha Salisu
Wata mummunar gobara da ta tashi a ranar Asabar ta lalata gidaje huɗu daga cikin biyar na gidajen kwana masu ɗakuna uku da ke kan titin Nelson Mandela, Asokoro, Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne daga na’urorin hasken rana (solar panels) da aka girka a saman rufin ɗaya daga cikin gine-ginen, kafin ta bazu zuwa sauran gidajen da ke kusa.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, Shugabar Hulɗa da Jama’a ta Sashen Kula da ibtila’i na Tarayya (FEMD), Nkechi Isa, ta ce kadarar da abin ya shafa mallakin tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, Sanata Ahmed Yerima.
Isa, tana ambaton Shugaban Tawagar Bincike da Ceto ta FEMD, Monday Addie, ta ce an samu rahoton lamarin ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Asabar. “Ba a rasa rai ko guda ba a wannan gobara.
Sai dai gidaje huɗu daga cikin biyar sun ƙone ƙurmus,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa an lalata kayayyakin amfanin gida da dama, ciki har da kayan ɗaki, tufafi, kayan abinci da sauran muhimman kayayyakin gida.
Jami’an agaji daga FEMD, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Hukumar Kashe Gobara ta FCT, Hukumar Kula da ibtila’i ta Ƙasa (NEMA), da Rundunar ’Yan Sandan FCT sun kai ɗauki wurin, inda suka samu nasarar shawo kan gobarara
StentorNews Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t