Ibtila’i! Tsutsa Ta Janyo Mana Asarar Naira miliyan 500. In ji Manoman Tumatur A Kano

Screenshot 20240416 094549 Facebook

Wasu manoman tumatur a karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano, sun koka kan yadda tsutsa ke lalata musu amfanin gona.

Alfijir Labarai ta rawaito manoman sun ce sun yi asarar amfanin gona da ta kai kusan Naira miliyan 500. Sun kuma ce tsutsar ta shafi kusan hekta 1000 na gonakinsu.

Wani manomin tumatir, Bello Idris ya ce suna cikin wahalhalu kan yadda tsutsar ta addabe su.

”Za mu nome tumatir mu sayi taki 50,000, mu kuma sayi maganin feshi 10,000 da man fetur amma duk a banza,” in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki da kuma gano inda matsalar take.

Haka-zalika, shi ma Sama’ila Bello mazaunin karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce tsutsar na lalata musu amfanin gona cikin lokaci kankani.

“Muna so gwamnati ta taimaka mana a duba a ɓangaren iri ne ko maganin feshi ne ba a sayar da mai kyau,” in ji Bello.

Daily Nigerian/BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *