Ibtila’i! Wani Mummunan Hatsari Ya Kashe Mutane 3, Ya Raunata Wasu 15

Screenshot 20231015 121421 com.whatsapp edit 5503044165826

Mutane uku ne suka mutu nan take yayin da 15 suka samu raunuka a wani hadarin mota da ya rutsa da wata motar bas ta kasuwanci da wata babbar mota a jihar Legas.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas ta bayyana hakan a ranar Lahadi, a wata sanarwa da babban sakataren hukumar Olufemi Oke-Osanyintolu ya fitar.

Osanyintolu ya ce lamarin ya faru ne a Gbagada, ta tashar motar Charlie Boy ranar Asabar.

Ya ce wata farar motar bas mai dauke da fasinja 18 mai lamba JJJ-844YA, birki ya shanye direban ya kasa tsaida mota, sai ta yi cikin wata motar da ke tafiya.

“Bayan kiran wayat su da aka samu da karfe 22:01 na safe ta layukan hukumar, LASEMA jami’an mu na ba da agajin gaggawa na jihar Legas sun isa wajen da karfe 22:17 na safe.

“Da isar jami’an mu wurin, an ga wata farar motar bas ta kasuwanci ta rasa yadda za ta yi, ta fada kan wata babbar motar da ke tafiya.

“Bas din kasuwanci mai dauke da fasinjoji 18, mai lamba JJJ-844YA kuma dauke da kaya, ta nufi Ajah daga Oshodi.

Ta rasa yadda za ta yi yayin da take tafiya, inda ta kutsa cikin wata babbar mota daga baya kuma mutane uku sun mutu nan take.

“Maza biyu da mace daya, dukkanin manya sun mutu nan take sakamakon lamarin, yayin da wasu suka sami nau’ikan raunuka daban-daban,” in ji shi.

Ya bayyana cewa daga cikin mutane bakwai da suka jikkata, uku an basu kulawa nan take kafin a kai su babban asibitin Gbagada domin ci gaba da kula.

“An kwashe gawarwakin ukun an kai su dakin ajiye gawa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *