Ibtila’In ya faru ne a yau ranar Lahadi,in da gobara ta tashi a gidan karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, da ke Asokoro.
Alfijir labarai ta rawaito mukaddashin Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Babban Birnin Tarayya Abuja, Amiola Adebayo, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Adebayo ya bayyana cewa gobarar ta kone bene na farko na ginin gaba daya.
Ya kara da cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9:45 na safe, sai dai ya ce jami’an hukumar sun isa wurin ne ‘yan mintoci kadan bayan da suka samu kiran gaggawa daga gidan ministar.
“Dukkan su suna kasan benen ba su san cewa wutar ta tashi ba, don haka basu sanar da hukumar kashe gobara akan lokaci ba. Duk da cewa sun ce sun kira layinmu bamu daga ba, amma dai mu kawai kiran gaggawa ne ya shigo mana”.
“Da isa wurin, sai muka ga cewa bene na farko na ci wuta. Don haka abin da za mu iya yi shi ne kawai mu hana wuta yadawa zuwa sauran sassan gidan, da kuma gine-ginen da ke kusa. Da kuma tabbatar da cewa ba a rasa rayuka,” in ji shi.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba, ko da yake mai taimaka wa ministar harkokin yada labarai Austin Elemue shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.



Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇