Ibtila’i! Yan daba sun sarewa wani dan kwamiti hannu a kano

📸Alfijir Labarai

Kwamanda ya kara da cewa wajen karfe biyu na dare suka sake dawowa,inda suka biyo bango suka zo suka afka mana har suka illata uku daga cikinmu.

Alfijir labarai ta rawaito Lamarin ya faru ne da misalin biyu na daren jiya inda yan dabar, su kimanin 30 suka afkawa ‘yan kwamitin,inda suka jikkata mutum 3 ciki harda Abdullahi yusif maitama da suka sarewa hannu gaba -daya, a unguwar kankarofi dake cikin birnin kano.

Shugaban kwamitin unguwar ta kankarofi, Ibrahim Garba Al muharram kankarofi ya yi wa tashar GTR HAUSA karin bayani akan lamarin, inda yace shigowar ‘yan dabar biyu a daren jiya.

”Na farko sun zo da misalin karfe goma na dare suka kwatarwa mutane wayoyi kuma suka farfasa motoci,kafin a sami nasarar korarsu da taimakon ‘yan sandan kwalli”.

Kwamanda ya kara da cewa wajen karfe biyu na dare suka sake dawowa,inda suka biyo bango suka zo suka afka mana har suka illata uku daga cikinmu.

A karshe yayi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, dasu kawo musu dauki akan wannan lamari, domin bi musu hakkin su dama hukunta wadanda sukayi musu wannan danyen aiki,tunda an san ko su waye.

Mun kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar kano SP Abdullahi haruna kiyawa amma bai samu daga wayar ba, haka zalika mun tura masa sakon karta-kwana amma shima bai dawo mana da amsa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *