Idan Ana Dara! Wani Gardi Da ke Shigar Fatima Mai Zogale Yana Damfarar Samari Ya Hadu Da Fushin Wani Alkali

FB IMG 1714583859248

Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba 1 a jihar Bauchi karkashin mai Shari’a Malam Ibrahim Jibo ta tura wani matashi Kabiru Ibrahim gidan Yari har zuwa 30 ga watan Mayun da muke ciki.

Alfijir Labarai ta rawaito an tuhumi matashin da yin shigar mata da sunan shi ne Fatima Mai Zogale yana yaudarar samari, inda dubunsa ta cika a lokacin da wani matashi ya dauke shi suka tafi kwanan gida.

Matashin ya amsa laifinsa na take, Kotun ta tura shi ajiye har zuwa ranar da za a ci gaba da shari’ar.

Daukakar Fatima mai Zogale ta zo ne bayan da shaharren mawakin nan Rarara ya wake ta.

Freedom Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *