IGP! An Kafa Wata Rundunar Tsaro Ta Musamman A Jihar Filato

FB IMG 1704172084914

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kaddamar da wata runduna ta musamman da za ta yi yaki da batagari da ke kashe-kashen rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Filato.

Alfijir labarai ta rawaito Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun wanda ya kai ziyarar gani da ido kan asarar rayuka da dama a wasu kananan hukumomin jihar Filato, ya ce rundunar ta musamman da gwamnatin tarayya ta amince da kaddamarwa a jihohi goma na Najeriya, zata fara aiki ne nan take a jihar Filato.

Tuni da mataimakin Sufeta Janar na shiya ta hudu, Ebong Eyibio ya kaddamar da jami’an runduna ta musamman zuwa yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaron.

A ci gaba da neman mafita kan batun kalubalen tsaron, Sanata mai wakiltar tsakiyar Filato, Diket Plang ya gabatar da wassu batutuwa a gaban majalisar dattawan, da ya ce za su taimaka wajen kawo dawwamammen zaman lafiya a jihar.

Sanata Diket Plang ya koka kan yadda maharan su dari hudu suka ratsa wurare suka mamaye kauyuka fiye da ishirin ba tare da wani ya gansu ba.

Ya kuma koka kan yadda wasu ke mamaye gonaki da gidajen wadanda suka yi gudun hijira, tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da jami’an tsaro na dindindin a yankunan.

A cewar Dah Mai’anguwa, Jamok Mafwalal Machambe daga gundumar Butura a karamar hukumar Bokkos, sun yi na’am da zuwan jam’an tsaron, ya kuma bukaci jama’a su basu goyon baya don samar da tsaro.

Sakataren kungiyar miyetti Allah a karamar hukumar Barkin Ladi, Abubakar Gambo yace suna bukatar jami’an tsaron su yi adalci.

A kokarin masu ruwa da tsakin na lalubo hanyoyin samun mafita kan lamarin tsaron, tambayoyin da ke bakunan al’ummar Filato sune, su wanene ke aikata kashe-kashen, daga ina suke fitowa, me suke bukata, wanene ke ba su makamai da sauran kayan aiki, yaushe ne za su kammala aikin nasu? Lokaci zai bayyana abin da ke faruwa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *