Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano, ta yi nasarar kammala rantsar da sabbin dalibai 1,380 da suka samu gurbin karatu na shekarar 2023/2024.
Alfijir labarai ta rawaito bikin rantsar da daliban karo na uku, ya gudana ne a ranekun Juma’a 2 ga Fabrairu da Asabar 3 ga Fabrairun 2024 a tagwayen dakin taro na Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, inda baki da aka gayyata, ciki har da iyaye da sauran abokan arziki suka halarci taron.
Bikin rantsarwar na kwanaki biyu ya fara ne da daliban Makarantun Shari’a da Kimiyyar Zamantakewa da Gudanarwa a rana ta farko, a yayin da daliban Makarantun Kwamfuta, Kimiyyar Lafiya da Kimiyyar Jinya aka rantsar da su a rana ta biyu.
A nasa jawabin shugaban jami’ar MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya ce taron alama ce ta rantsar da daliban da suka samu gurbin karatu a jami’ar a hukumance, kamar yadda hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta amince da su.
Ya taya daliban murnar samun damar shiga jami’ar sannan ya bukace su da su rungumi kyakkyawan tarbiyya da kuma fuskantar karatunsu da gaske.
“Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya a Kano, yanzu ta fadada. Tana da hangen nesa na ganin ta bayar da abu mai inganci a fannin bincike, isar da abu a fannin kimiyya, shugabanci da gudanarwa.
“Fatan Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya a Kano, yana da girma. Ina mai kira ga kowa da kowa da ya hada kai da wanda ya assasa wannan jami’a da tawagarsa na kwararrun malamai da masana domin ganin ci gaban Jami’ar tare da kara fadada ta,” in ji shi.
Ya ce jami’ar tana karantar da kwasa-kwasai wadanda kawai da ke da kimar kasuwanci ga dalibai, yana mai jaddada cewa tsarin koyarwa a jami’ar ya shafi sanyawa dalibai sha’awar harkokin kasuwanci da hanyoyin dogaro da kai.
A nasa jawabin, wanda ya kafa gamayyar jami’o’in MAAUN kuma shugaban jami’o’in, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ce MAAUN jami’a ce ta duniya domin akwai dalibai daga wasu kasashe ciki har da kasar Sin.
Ya shawarci daliban da aka rantsar da su fuskanci karatunsu da gaske, inda ya ce duk wanda ya kasa to za a nuna masa hanyar barin jami’ar.
Ya ce ya kamata sabbin daliban su yi wa kan su murna na samun gurbin shiga jami’ar inda ya ce, domin shaidar kammala karatu a jami’ar ta MAAUN an amince da ita a kasar Amurka.
Farfesa Gwarzo ya ce ya kamata daliban da suka samu gurbin karatu su kuma yi alfahari da kasancewarsu na shiga cikin iyalin MAAUN domin ya ce za su ci dimbin gajiyar jarin ilimi da na abin duniya.
Ya ce jami’ar ta himmatu wajen samar da ilimi mai inganci domin samar da kwararrun daliban da za su bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban nahiyar Afrika da ma duniya baki daya.
A sakon sa na fatan alheri, mataimakin shugaban jami’ar Franco-British International University (FBIU) a Kaduna, Farfesa Abdullahi Mohammad Sabo ya shawarci daliban da su tsara manufarsu tun daga ranar nan da aka rantsar da su domin su kammala karatunsu da sakamako mafi kyawu.
Ya kuma hori daliban da aka rantsar da su kasance masu kyakkyawan hali domin kiyaye sunan Jami’ar tare da cimma burinsu na rayuwa.
Shima a sakon sa na fatan alheri, mataimakin shugaban jami’ar MAAUN Maradi, Dakta Shu’aibu Tanko ya ce tasirin MAAUN ba kawai a iya karatu bane har ma da zuba ma basirar da za ta bai wa dalibai damar dogaro da kai bayan kammala karatunsu.
“Kun zo nan ne don samun mafi kyawu domin ku tsaya da kafafunku bayan kammala karatu,” in ji shi.
Shima a sakon sa na fatan alheri, Mataimakin Shugaban Jami’ar NorthWest Sakkwato, Farfesa Ahmad Maigari Ibrahim wanda ya samu wakilcin Dr Rabi’u Muhammad ya shawarci daliban da suka samu gurbin karatu da su guji yin abubuwan da za su iya bata sunan su da na jami’ar.
Mataimakin shugaban jami’ar MAAUN Kano bangaren gudanarwa, Dakta Habib Awais Abubakar wanda ya jagoranci gabatar da rantsarwar a lokacin bikin rantsar da daliban, shi ne ya rantsar da sabbin daliban.
Sauran ma’aikatan Gudanarwa da suka halarta a yayin bikin sun hada da; Mataimakin Jami’ar bangaren rayuwar makaranta (Campus Life), Dr. Hamza Garba da Daraktan Tsare-tsare na ilimi da tabbatar da inganci, Dr. Nura A. Yaro.
Sauran sun hada da Shugaban ofishin huldar kasa da kasa na MAAUN (International Office), Engr. Bashir Garba, Shugabannin Makarantu, Shugabannin sashe, Jami’an tsaro da kuma baki da aka gayyata da dai sauransu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V