Inec ta bayyana Usman Ododo na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kogi

📸Ododo

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta bayyana Usman Ahmed Ododo na jam’iyyar APC a matsayin wanda lashe zaɓen gwaman jihar Kogi na shekara ta 2023.

Alfijir Labarai ta rawaito babban jami’in tattara sakamakon zaɓe na hukumar INEC a jihar Kogi, Johnson Ozoemenam Urama ne ya tabbatar da nasarar ta Ododo a sanarwar da ya bayar cikin daren ranar Lahadi.

INEC ta ce Ododo na APC ya samu ƙuri’a 446,237, saboda haka shi ne halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar, kasancewar shi ne ya samu ƙuri’a mafi rinjaye.

Muritala Yakubu Ajaka na jam’iyyar SDP shi ne ya zo matsayi na biyu, inda ya samu ƙuri’a 259,052.

Dino Melaye na jam’iyyar PDP ne ya zo na uku da ƙuri’u 46,362.

Sai kuma Abejide Leke Joseph na jam’iyyar ADC wanda ya samu ƙuria 21,819.

Gabanin sanar da nasarar Ododo, hukumar zaɓen ta ce ba za a gudanar da zaɓuka a rumfunan da ta dakatar da zaɓe ba a ranar Asabar.

An dakatar da zaɓe a wasu rumfuna ne bayan samun bayanai na almundahana, inda aka ga cikakkun takardun sakamako tun gabanin fara kaɗa ƙuri’a.

Sai dai a bayanin da jami’in hukumar INEC ya yi gabanin sanar da wanda ya yi nasara, ya ce yawan katin zaɓe da aka karɓa a dukkanin wuraren da aka soke zaɓe ya tsaya ne a 16,247.

Hakan na nufin koda an sake zaɓen ba zai shafi nasarar ɗan takarar da ke gaba a yawan ƙuri’a ba.

Ahmed Ododo ya bai wa mai biye masa ratar ƙuri’a 187,185.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *