Allah ya yiwa mahaifiyar tsohon Shugaban Kungiyar masu Shirya Fina finai ta Jihar Kano, Alhaji Sa’idu Isah Gwanja, wadda kuma ita ce kishiyar mahaifiyar mawaki Ado Isah Gwanja.
Hajiya Binta rasuwa a yau Talata bayan ta karya kumallo sai ta koma barci, har lokacin tashin barcin ya yi aka ba ba ta tashi ba.An tabbatar da rasuwarta ne da misalin karfe 12:38 na rana.
Hajiya ta rasu ne tana da shekara 82, a gidan da ake Naibawa Layin Danhassan cikin garin Kano, ta bar ‘ya’ya biyu, Sa’idu da kanwar sa.
An yi jana’izar ta a unguwar Fagge cikin garin Kano. Muna Addu’ar Allah ya jikan ta, ya bawa yaya da iyalanta hakurin rashinta amin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL