Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Allah Ya Yiwa Dan Majalisar Wakilan Najeriya Rasuwa

FB IMG 1715334396580

Allah ya yi wa ɗan Majalisar Wakilan Nijeriya Hon. Isa Dogonyaro rasuwa yau Juma’a.

Marigayin shi ne yake wakiltar mazaɓar Garki da Babura daga jihar Jigawa a Majalisar Wakilan Nijeriya.

Wata sanarwa da shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar Akin Rotimi ya fitar ta ce marigayin ya rasu ne da safiyar Juma’a a Abuja, yana da shekara 46.

Sanarwar ta ce Hon. Isa ya bar mata da ‘ya’ya.
Za a yi jana’izarsa a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, bayan sallar Juma’a.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *