Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Allah Ya yiwa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba

 Innalillahi wa inna ilaihirraji un. 
Allah Ya yiwa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Best Seller Channel 
b

  BBC ta rawaito Abdul Amart Mai kwashewa ya sanar dasu Rasuwa Sani Garba S k Jarumi a masana antar Kannywood. 

Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma.

Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe sati biyar yana jinya a asibitin,” 

Best Seller Channel 

Tun asali cutar ciwon suga ce yake fama da ita, wacce daga bisani ta haifar masa da cututtuka irinsu ƙoda da hanta da hawan jini.

“A ranar yau da ya rasu ɗinnan aka fara yi masa wankin ƙoda,” a cewar Furodusa Amart, wanda shi ke tsaye a kan kula ɗaukar nauyin kula da lafiyar marigayin.

Best Seller Channel 

SK ɗan asalin unguwar Zage ne a cikin birnin Kano, kuma a baya kafin ya fara harkar fina-finai mai yabon Manzon Allah ne a ƙungiyar Usha’un Nabiyyu.

 Za  a yi jana’izarsa a gobe Alhamis,  muna addu ar Allah ya gafarta masa Allah ya shafe kura kuransa Allah ya Bawa iyalansa hakurin rashisa. 

Slide Up
x