Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi rashin kawunsa, Alhaji Hassan Yusuf Danmakwayo.
Alfijir labarai ta rawaito wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan jihar, Marigayi bayana rasuwar.
Hassan Yusuf ya rasu bayan ya sha fama da jinya, ya rasu Yana da shekaru 72, ya rasu ne a ranar Asabar kuma an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Marigayi ya rasu ya bar matarsa da ’ya’ya da yawa da jikoki da ‘yan uwa. Dan’makwayo ya kasance kanin marigayi Alhaji Kabir Yusuf, mahaifin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Muna addu ar Allah ya jikansa da rahama Allah ya bawa iyalansa hakuri
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl