Jami’ar Bayero Ta Kara Kuɗin Makaranta Da Dakunan Kwanan Ɗalibai

Jami’ar Bayero da ke Kano ta kara kudin makarantar sabbi da kuma tsofaffin dalibai masu karatun digiri na farko da na biyu.

Alfijir Labarai ta rawaito Jami’ar Bayero ta wallafa wata sanarwa a shafinta na Facebook dauke da bayanai kan yadda karin kudin makarantar ya shafi tsangayoyin karatu daban-daban.

Hakan na zuwa ne makonni bayan gwamnatin Nijeriya ta sanar da fito da tsarin bai wa dalibai bashin kudin karatu mara kudin ruwa, wanda tun a lokacin aka soma hasashen cewa za a yi karin kudin makaranta a fadin kasar.

Jami’ar ta bayyana cewa karin zai fara aiki ne a zangon karatu na 2022/2023.

Yadda tsarin zai kasance shine:

Daliban tsangayoyin koyar da Fasaha da Addinin Musulunci da Shari’a da Ilimin Zamantakewa da Kimiyyar Gudanarwa za su rinka biyan naira 95,000 a matsayin kudin makaranta a duk shekara sa’annan sabbin dalibai a tsanagayoyin za su biya naira 105,000.

Tsangayoyin koyar da Aikin Banki da Hada-Hadar Kudi da Lissafin Kudi za su koma biyan naira 97,000 inda sabbin dalibai kuma su biya naira 107,000.

Tsangayoyin koyar da Ilimin Kwamfuta da Sadarwa da Kasa da Muhalli za su rinka biyan naira 100,000 sai kuma sabbin dalibai su biya 110,000.

Tsagayar koyar da Ilimin Sinadaren Kasa da kuma tsangayar koyar da Tsara Taswirar Birane za su koma biyan naira 105,000 sa’annan sabbin dalibai su biya naira 115,000.

Baya ga kudin makaranta, Jami’ar ta kara kudaden da ake biya na dakunan kwanan dalibai.

A cewar sanarwar, dakin dalibai maza mara gado da katifa ya koma naira 37,590, sai kuma daki mai gado da katifa 57,590.

Hakazalika dakin dalibai mata mai gado da katifa ya koma 80,090.

Sa’annan dakin kwanan dalibai na mata ‘yan Nijeriya masu digiri na biyu ya koma naira 200,000, sai kuma na mata wadanda ba ‘yan Nijeriya ba ya koma 200,000.

Dakin maza kuwa ‘yan Nijeriya masu digiri na biyu ya koma naira 150,180 sai kuma wadanda ba ‘yan Nijeriya ba 300,000.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Jami’ar Bayero Ta Kara Kuɗin Makaranta Da Dakunan Kwanan Ɗalibai”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *