Gwamnatin Kano Zata Sake Gina Ginin Da Ta Rushe A Shataletalen Gidan Gwamna

Gwamnatin Kano zata sake gina ginin da ta rushe a shataletalen kofar gidan gwamnatin jihar

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan bayan da ya gana da wadda ta kirkiro taswirar zanen ginin Kaltume Gana.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Hisham Habib ya fitar, ya ƙara da cewar yanzu haka gwamnatin zata yi sabon ginin a Fly Over ta Naibawa.

Gwamnan yace bayan sun yi bincike, sun gano cewa wurin da za’a sake ginin nan ne ya fi dacewa, inda bazai yi barazanar ga masu wucewa da ababan hawa ba.

Wadda ta zana ginin Kaltume Gana ta gode wa gwamnan akan wannan ƙudurin nasa, kasancewar bai bari tayi wahala a banza ba.

An dai zana ginin domin murnar cikar Kano shekara 50 da kafuwa lokacin tsohon gwamnan Ganduje.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *