Jam’iyyar APC ta yi martani tare da caccaka ga Atiku Abubakar

FB IMG 1696596268908

Atiku Abubakar, Yace Sakamakon shari’ar da Kotun koli zatayi wa shugaban kasa, Bola Tinubu ne kawai zai kawo ƙarshen Takaddamar Siyasar da shugaban kasa.

Alfijir Labarai ta rawaito tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na ƙasa da ƙasa a Abuja Ranar Alhamis, Bayan da ya Karɓi Takaddun Karatun Shugaba Tinubu daga jami’ar jihar Chicago (CSU).

Atiku ya kuma bayyana cewa ya hana wakilan shugaba Tinubu shiga Gidansa jim kaɗan bayan zaɓen Shugaban ƙasa da aka Gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023. Rahotanni sun bayyana cewa tawagar ƙarƙashin Jagorancin Gwamnonin APC na yin aiki ne bisa ga umarnin shugaban kasa, Inda ya bukaci Atiku ya amince da shan kaye.

Atiku ya ce baya tsoron kada a ka tsaye masa sha’anin kasuwancinsa Sakamakon Kalubalantar Nasarar zaɓen Shugaban ƙasar. Ya yi nuni da cewa, tun daga lokacin da aka kwace masa lasisin shigo da kayan masarufi, Wadda ita ce babbar sana’ar da ke da wani nau’i na Gwamnati a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki a shekarar 2015.

“Ba na tsoron a Dakile A kasuwancina in ji Atiku. “Bana yin wani aikin Gwamnati, zan bar wannan fada ne kawai idan Kotu ta yanke hukunci, Muna Kotun koli.”

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewa ya dauki wannan tafiya ne domin bankaɗo Ɗimbin cece-kuce da suka dabaibaye shugaban kasa Bola Tinubu, Domin ya zama wani ɓangare na manyan batutuwan da suka bayyana makomar Gwamnatin Zaɓaɓɓen shugaban kasa da halaccin Shugabanci a Najeriya.

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, ta caccaki Atiku kan laifin da ya yi wa Tinubu a fannin karatunsa, Duk da furucin da CSU ta yi cewa Tinubu ya halarci makarantar kuma ya kammala karatunsa.

Jam’iyyar APC ta zargi Atiku da cewa ya yi kaurin suna da ƙoƙarin bata Sunan shugaba Tinubu.

Jam’iyyar ta kuma Buƙaci Atiku da ya Amince da shan kaye

Sai dai Atiku ya sha alwashin ci gaba da fafatawa har sai kotun koli ta yanke hukunci a kan shari’ar sa. Ya ce yana da yakinin cewa kotu za ta wanke shi kuma ta yi watsi da Nasarar da Tinubu ya samu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *