.
Alfijr
Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta tabbatar da mutuwar ɓarawon kayan taransifoma bayan da wuta ta ja shi a kauyen Amoji-Ukwu da ke Ƙaramar Hukumar Obingwa a jihar Abia.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna, ya bayyana cewa, wanda ake zargin ɓarawo ne da har ya yanke wayoyi biyu a jikin na’urar ta taransifoma da sanyin safiyar Juma’a, kamar yadda ya tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a ranar Asabar a Aba.
Alfijr
Wani mazaunin kauyen Amoji-Ukwu, Chinenye Agomuo, ya bayyana cewa, an ji ƙarar fashewar wani abu a ranar Juma’a, kuma lamarin ya faru ne lokacin da wani mutum ya yanke wayoyi a jikin taransfoma.
Da safiyar Juma’a, da misalin karfe 4:00 na safe, mun ji karar fashewar wani abu da ake zargin na’urar taranfoma ce.
“Bayan fashewar, na fara samun kiran waya daga dan uwana da ke zaune kusa da tiransfomar, yana neman in zo wajen da abin ya faru.
Alfijr
“Ya ce wani ne ya hau taransfoma sai wutar lantarki ta kama shi.
“Lokacin da muka isa wurin, sai muka ga ashe matashi ne.
Agomuo ya ce “Ya haura cikin taransifomar ne don yanke wayoyi, inda a hakan ne sai wutar ta kama shi ya mutu,” in ji shi.
Ya ce al’ummar yankin sun kai rahoton faruwar lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda na Gabashin Ngwa.
Alfijr
Agomuo ya ce an ajiye gawar wanda ake zargin a mutuware tare da taimakon ‘yan sanda.
Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa