Kalubale ga manya arewa! malamai da yan siyasa da sarakuna – Barr Bulama bukarti

FB IMG 1696321252328

Sarakunan gargajiya sun kasa tashi suyi abinda ya dace , malaman addini sun kasa tashi abinda ya dace suyi , yan siyasa sun kasa tashi suyi abinda ya dace suyi to yaya za’a yi kenan.

Alfijir Labarai ta rawaito cikin shirin fashin baki na su Barrister Audu Bulama Bukarti da kuma sauran abokansa Ja’afar Ja’afar da kuma barrister Abba hikima tare da Nasiru zango.

Barrister Audu Bulama Bukarti yayi magana ne akan sace yan matan jami’ar tarayya ta Gusau a jihar Zamfara

Idan gwamnatin tarayya batayi wani abu ba, shin munga gwamnan jihar Zamfara ya tafi gurin shugaban kasa tunda yaran nan a garin Gusau aka dauke su.

Ko gwamna zamfara bashi da hakki ne zuwa inda shugaban kasa idan kace adawa ce lokacin da aka kai hari a Maiduguri, Kashim yaje gaban shugaban kasa yana kuka da hawaye akan abinda yake faruwa a Maiduguri shi gwamnan Zamfara me yake yi.

Barrister majalisar Yan majalisu bata ce komai ba shi dan majalisar mai wakilta wajen yace wani abu, basu da sanata ne yace wani abu me sukeyi menene amfaninsu ?.

Sarakunan gargajiya sun kasa tashi suyi abinda ya dace , malaman addini sun kasa tashi abinda ya dace suyi , yan siyasa sun kasa tashi suyi abinda ya dace suyi to yaya za’a yi kenan.

Ya kamata kowace kungiya addini su tsaya suyi magana akan a dawo da tsaro a yankin arewa, idan sun yi dan Allah suka dogara ga Allah to gwamnatin tarayya zata saurare su kuma za’ayi abinda ya dace.

Yan majalisa da sarakuna basu da amfani idan basu tashi sun yi wani abu ba, wannan maganar tana daga cikin rashin tsaron da aka samu a cikin wannan mako da muke ciki yanzu yawan mutanen da ke hannun yan bindiga Allah ne Kaɗai yasan yawan su.

Ga vvideo din 👇👇👇

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *