Daga Aminu Bala Madobi
Bayan Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya dakatar da kasar Gabon kan hambarar da gwamnatin shugaba Ondimba Ali Bongo a ranar Laraba da sojoji karkashin jagorancin shugaban masu gadin ‘yan Republican, Gen Brice Nguema suka yi.
Alfijir Labarai ta rawaito Kungiyar kasashen nahiyar a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, 2023, a wani sakon da ta wallafa a shafin X, ta yi Allah wadai da kwace mulki da sojoji suka yi a kasar da ke tsakiyar Afirka.
Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da kasashen Rwanda da Kamaru suka yi gaggawar sallamar manyan hafsoshi sama da 1000 a wani mataki na ba-zata a kan sojojinsu.
Hukumomin kasar Rwanda sun amince da murabus din wasu janar-janar guda 12 da suka hada da wasu janar-janar guda hudu James Kabarebe da Fred Ibingira da wasu manyan hafsoshin soja guda biyu Charles Kayonga da Frank Mushyo Kamanzi da wasu jami’ai da dama.
A cewar wata jaridar kasar Rwanda, News Times, gwamnatin kasar ta amince da murabus din wasu janar-janar guda 12 da wasu hafsoshi da dama. Sanarwar ta bayyana cewa an sanar da ritayar ne a ranar Laraba, a cikin wata sanarwa da rundunar tsaron kasar ta Rwanda ta fitar.
A Kamaru, shugaban kasar Paul Biya ya kuma yi wa sojoji garambawul tare da sabbin nade-naden mukamai a rundunar sojin kasar Controle Generale des Armee.
Sojoji a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis sun nemi tabbatarwa masu ba da gudummawa na kasa da kasa cewa za su mutunta duk alkawurran da aka yi a gida da waje da kuma “tsakanin” cibiyoyin rikon kwarya.
Kakakin sabuwar gwamnatin, Col Ulrich Manfoumbi, ya fadawa gidan talabijin na kasar cewa za a rantsar da Nguema a kotun tsarin mulkin kasar aranar litinin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
Ina gamsuwa kwarai da labaranku da fatan Allah ya kara maku kwarin fwiwa,ta taimaki Alfijir Amin
Ameen ameen muna godiya
Ina gamsuwa kwarai da labaranku da fatan Allah ya kara maku kwarin gwiwa,ya taimaki Alfijir Amin