Kamfanin Mai Na NNPCL Ya Bayyana Dalilan Da Ya Jawo Ƙarancin Fetur A Najeriya

IMG 20231119 140840

Kamfanin man fetur na gwamnatin Najeriya NNPCL ya ce ambaliyar ruwa da kuma rashin kyawun yanayi ne suka jawo tsaiko wajen jigilar man a Abuja da wasu jihohin ƙasar.

Alfijir labarai ta ruwaito tun a makon da ya gabata ne aka fara ganin dogayen layuka a ƙofar gidajen mai na Abuja babban birnin ƙasar da kuma wasu jihohi, inda masu ababen hawa kan shafe awanni kafin su sha man.

Wata sanarwa da NNPCL ya fitar ta ce “hakan ta faru ne sakamakon matsalar jigilar sauke man daga manya zuwa ƙananan jiragen ruwa na dako”.

“Haka nan, saboda hatsarin da ke tattare da fetur da kuma bin umarnin hukumar kula da yanayi cewa kada a yi jigilar mai yayin da ake tsaka da kwarara ruwan sama da tsawa, ba zai yiwu a yi lodin mai ana tsaka da tsawa da walkiya da kuma shatata ruwa ba,” in ji sanarwar.

“Bugu da ƙari, matsalar ta ta’azzara ne saboda ambaliya ta mamaye wasu hanyoyin manyan motoci, abin da ya jawo tsaiko a jigilar man daga tashohin ruwa zuwa Abuja.”

Zagayen da wakiliyar BBC ta yi a wasu gidajen man tsakiyar birnin na Abuja ya nuna akan sayar da lita ɗaya tsakanin N700 zuwa naira N750, saɓanin N617 zuwa 690 da aka sayar da shi a farkon makon da ya gabata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *