Kamfanin Twitter Na Barazanar Maka Meta A Kotu Kan Satar Fasaha

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin Twitter na barazanar kai karar Meta kan “Shirin kwaikwayan fasahar Sada zumunta, da gangan ba bisa ka’ida ba” na sirrin kasuwanci na Twitter da Internet Protocol (I.P)

Alfijir Labarai ta rawaito cewa kamfanin na kafofin watsa labarun yana kuma barazanar kai karar Kamfanin Meta don soke bayanan Twitter da satar fasaha.

An bayyana hakan ne a wata wasikar tsagaitawa da hani da lauyan Elon Musk Alex Spiro ya aikewa Mark Zuckerberg ranar Laraba.

An tattaro cewa zargin ya shafi sirrin kasuwanci da tsofaffin ma’aikatan Kamfanin Twitter Wanda Kamfanin Meta suka dauka aiki ne suka Bada bayanan amma kuma ya nuna cewa Meta na iya goge bayanan Twitter wanda ya saba wa ka’idojin sabis.

Da yake tabbatar da rahotannin karar da ke tafe, mai shafin Twitter, Elon Musk ya rubuta a shafinsa na sada zumunta: ” ‘cewa Ayi gasa dai dai ne ba satar fasaha ba’

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *