Daga Aminu Bala Madobi
Duk da dokar hana fita ta awanni 24 a jihar Kano, wasu masu zanga-zanga sun fantsama kan tituna a ƙaramar hukumar Minjibir domin nuna damuwarsu kan matsin tattalin arziki da ake ciki.
Alfijir labarai ta ruwaito rahotanni sun bayyana cewa masu zanga zangar na dauke da kwalaye da aka rubuta korafe korafensu daban-daban.
Wani mazaunin yankin, Tasiu Minjibir ya shaidawa jaridar Vanguard cewa masu zanga zangar sun yi ta cikin lumana a karamar hukumar.
Ya ce masu zanga zangar na neman a dawo da tallafin man fetur.
A jiya ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar hana fita ta awanni 24 bayan bata gari sun kutsa cikin masu zanga-zanga.
VANGUARD
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj