Kasar Burtaniya Ta Haramtawa Ma’aikatan Lafiyar Najeriya Kawo ‘Yan Uwansu

FB IMG 1710173434944

Hukumomin Burtaniya sun haramta wa ma’aikatan kiwon lafiya shigo da ya uwansu da makusantan su kasar.

Alfijir labarai ta rawaito Ofishin cikin gida na Burtaniya ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin.

A cikin wani sakon twitter, Ofishin Cikin Gida na burtaniya ya rubuta cewa, “Daga yau, ma’aikatan kula da ke shiga Burtaniya kan takardar izinin Ma’aikatan Lafiya zasu kara Kulawa sosai domin dakatar da duk wani baƙon likita da yake kokarin kawo yan uwansa.

Yayin da yake bayyana manufarsu a cikin wata sanarwa ta daban, ya ce a shekarar da ta gabata kadai, jimillar ma’aikata 120,000 suka karu zuwa Burtaniya.

“Ayyukan gyare-gyare don hana ma’aikatan jinya kawo ‘yan uwa yanzu ya fara aiki, yayin da ake buƙatar likitocin su yi rajista idan suna tunanin zuwan baƙi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *