KATOBARA! Wani mutum ya yi yunƙurin kashe kansa a Masallacin Ka’aba

Screenshot 20240310 210256 com.facebook.katana edit 1808895184618

Jami’an tsaro na musamman da ke kula da Masallacin Harami sun fara gudanar da bincike kan mutum da ya yi yunkurin halaka kansa, inda ya hau bene na sama na Masallacin domin ya faɗo ƙasa.

Alfijir labarai ta rawaito an garzaya da mutumin zuwa asibiti domin samun kulawar da ta dace, sai dai ba a bayyana ƙasar da ya fito ba.

Rundunar ta musamman mai kula da tsaron masallacin Harami  ta bayyana a shafinta na X cewa “an kammala binciken da ya kamata,” amma babu wani ƙarin bayani kan lamarin.

A shekarar 2018, wani mahajjaci dan shekaru 26 ya kashe kansa a  Masallacin Haramin, lamarin da ya haifar da firgici da fargaba a tsakanin alhazai da masu ibada a Masallacin.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Makkah ya bayyana a watan Yunin 2018 cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike kan wa

ni lamari, inda wani mahajjaci ya yi tsalle daga kan wani rufi a unguwar Mas’a ya kuma faɗo ƙasa, abin da ya yi sanadiyyar rasa ransa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *