Komai Girmanka Indai ka Shigo APC a Karkashina Zaka Zauna – In Ji Ganduje

FB IMG 1695548443044

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa duk wani dan jam’iyyar APC a yanzu a karkashin sa yake saboda shi ne shugabanta na kasa a yanzu.

” Kada ka ji tsoro idan wani ya zo cin arziki a gidanka, shin da ka je kaci arziki a gidan shi da ya zo yaci arziki a gidanka wanne ka fi so? , Ai mai shi shi yake da abun bayarwa, marashi shi ne mai neman wurin shiga”.

Alfijir labarai ta rawaito Dr. Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da shugabannin kungiyoyin jam’iyyar APC a Ofishin Support Group dake Kano.

” Menene aikin shugaban jam’iyyar APC na kasa ? Aikine na jam’iyya a jihar kano kawai ? Jihohi 36 da Abuja duk inda naje nine yallabai nine alasabbanani, nine Sheikh, duk inda naje nina alangoburo, saboda haka na zaga kasar nan ina kiran gwamnoni su shigo jam’iyyar APC don mu samu karuwa, to meye laifi idan na yi haka a jihata ta kano?. Ganduje ya fada

Shugaban jam’iyyar Wanda tsohon gwamnan jihar kano ne ya ce ya sami nasarar shigo da ‘yan kananan jam’iyyu cikin har da NNPP a jihar Bauchi, “don haka a kano ma, Ina rokon yan Jam’iyyar NNPP dukkanin su da su ajiye kayan kwari su zo Inda za’a Adana musu shi a furji don kar su lalace”.

” Yanzu laifi ne Dan na kirawo yan Jam’iyyar NNPP na jihar kano su dawo APC, ai wanda yake da shi shi ake roko, wanda yake da shi shi yake bayarwa, saboda muna rokon su su auna cewa Shugabancin kasar nan a jam’iyyar zai samu?, To saboda kiransu su dawo jam’iyyar APC ai abun alfahari ne mu a wajen mu don haka mu kari muke nema, kuma kamar yadda na fada muku indai ka shigo jam’iyyar ko kai jagorane to nine shugabanka”.

Kadaura24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

One Reply to “Komai Girmanka Indai ka Shigo APC a Karkashina Zaka Zauna – In Ji Ganduje”

  1. Gaskiya ne wannan; amma yi ma gwamna magana ba tare da an tauna ta ba, kamar Kwankwaso haka ya inga yi ma mak girma Ganduje, a sanda ya na mulki; shi ya sa, ba zai yu shi kuma ya risinar da kai ga jam’iyyar adawa ba.
    A ganina Ganduje ya na yi ma gwamna iirin wannan kiran, don ya na tunanin dole gwamna zai biyo su, tun da har su ka bar ma sa kujerar gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *