Wata mata mai suna Rabi a birnin Kano ta fara girbar abinda ta Shuka sakamakon hukuncin da alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci ya yanke mata
BBC ta rawaito, bayan tabbatar da kama ta da laifin yi wa maƙociyarta ƙazafin bata suna da Kalmar “karuwanci” mai Shari’a Halhalatul Khuza’i ne ya tabbatarwa da Rabi mazauniyar Rijiyar Zaki da laifinta bisa shaidu, sannan ya yanke mata hukuncin Sha re titin unguwarsu baki ɗaya na tsawon kwana 30.
Malama Rabi ta ce ba ta da wani ƙorafi game da hukuncin, tana mai cewa ta ji daɗi da hukuncin bai wuce hakan ba.
Ta kuma ja hankalin masu irin wannan da su guji bata sunan mutane ba gaira ba dalili