Kotu Ta Dage ƙarar da aka Shigar Dake Neman A Cire Ganduje Daga Shugabancin jam’iyyar APC Na Ƙasa

FB IMG 1719477546654

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake dage sauraren karar da ke neman a tsige Dr. Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa har zuwa ranar 5 ga watan Yuli.

Alfijir labarai ta ruwaito Mai shari’a Inyang Ekwo ya dage ci gaba da shari’ar a ranar Larabar da ta gabata domin baiwa mai kara damar amsa sabuwar bukatar da Ganduje ya shigar, yana mai kalubalantar cancantar karar.

A yayin ci gaba da sauraron karar, lauyan mai kara, Benjamin Davou, ya shaida wa kotun cewa Sanusi Musa, SAN, mai wakiltar Ganduje, ya mika masa wata sabuwar bukata. ya bukaci lokaci don yin nazari kan kudirin da kuma yanke shawarar mayar da martani.

Sunusi Musa SAN bai yi adawa da bukatar Davou na dage zaman ba. Don haka mai shari’a Ekwo ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Yuli.

Wanda ya shigar da karar, kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya karkashin jagorancin Saleh Zazzaga, ya shigar da karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/599/2024. Suna kalubalantar nadin Ganduje a matsayin Shugaban jam’iyyar APC, suna masu cewa bai dace ba tunda shi ba dan shiyyar Arewa ta tsakiya ba ne.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Ganduje, APC, da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Mai shigar da karar na neman hana Ganduje ci gaba da rike mukamin Shugaban jam’iyyar APC, Sannan kuma kotu ta umurci INEC da kada ta amince da duk wani mataki da APC ta dauka da suka hada da ‘yan majalisa, ‘yan takara, da kuma nade-nade, tun bayan da Ganduje ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar a ranar 3 ga Agusta, 2023.

Wanda ya shigar da karar ya ce shugabancin Ganduje ya sabawa doka domin shi ba dan shiyyar Arewa ta tsakiya ba ne. Suna zargin cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa (NEC) ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar inda ta nada Ganduje daga jihar Kano a shiyyar Arewa maso Yamma don maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa a shiyyar Arewa ta tsakiya.

Mai shigar da karar ya bukaci a bayyana cewa, a karkashin sashe na 20 (1) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC na shekarar 2013 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima), ba za a iya nada Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar ba ba tare da an Gudanar da zaɓen dimokuradiyya ba, wanda hakan ya sa mukamin da yake a yanzu ya sabawa doka.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *