Kotu Ta Dakatar Da Gwamnan Sokoto Daga Tube Rawanin Hakimai

FB IMG 1719326255392

Babbar kotun jihar Sokoto ta dakatar da tube rawanin Hakimai guda 2 wanda hakan ke da alaka da kudurin dokar masarautu ta jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito babbar kotun ta bada umarnin dakatar da yunkurin Gwamna Ahmed Aliyu na cire Hakiman guda 2 cikin guda 15 da aka cire a baya.

Hakiman, Alhaji Buhari Tambuwal da Alhaji Abubakar Kassim ne suka shigar da karar.

Gwamnatin jihar dai ta sauke su daga mukamansu ne kan zargin rashin biyayya da kuma hannu da suke da shi kan matsalar tsaro a jihar.

Mai shari’a, Kabiru Ibrahim Ahmed ya umarci Gwamnan da Antoni Janar na jihar da fadar Sarkin Musulmai da su jinkirta yayin da za a saurari karar.

A ‘yan kwanakin nan dai ana ta yada jita jita kan zargin cewa Gwamnatin jihar Sokoto na shirin tube rawanin Sarkin Musulmai, sai dai gwamnatin ta musanta batun.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *