Kotu Ta Mayar Da ‘Yan Majalisar Rivers 25 Da Aka Kora Kan Kujerunsu

Screenshot 20240704 193235 Facebook

Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta soke hukuncin babbar kotun da ke zama a jihar Rivers, wanda ya kori Martin Amaewhule da wasu mutum 24 daga majalisar dokokin jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito kotun, wadda alaƙalanta uku suka yanke hukunci, ta ce ƙaramar kotun ba ta da hurumin yanke hukuncin.

Kotun ta bayyana cewa sashe na 271(3) na kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa babbar kotun tarayya ikon tantance ko za a ayyana kujerar ɗan majalisa a matsayin fanko.

A cewar kotun, ikon da kundin tsarin mulkin ƙasar ya bayar bai shafi manyan kotunan jihohi ba.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke cewa an soke hukuncin korar da aka yi ba tare da wata hujja ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *