Kotu Ta Rab Auren Ƴar Gwamnan Kano, Ga Yadda Ta Kasance

Alfijr ta rawaito Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano a ranar Alhamis ta raba auren Asiya Ganduje, diyar Gwamnan Jihar Kano, mai shekara 16 da yin sa.

Asiya ta garzaya kotu tana neman a raba aurenta da mijinta, Inuwa Uba, saboda ta gaji da zaman aure wanda suka haifi da ‘ya’ya hudu a zaman nasu.

Alkalin kotun, Khadi Halliru Aliyu ya raba auren ne a lokacin da yake yanke hukunci kan lamarin a ranar Alhamis.

Sai dai mai shari’a ya umarci diyar Ganduje da ta mayar wa mijinta Uba, sadakin N50,000 a matsayin asarar da ta yi.

Kotun ta kuma yi watsi da bukatar mijin Asiya na neman takardun kadarorin da ya ce nasa ne.

Lauyan wanda ya shigar da karar, Ibrahim Nassarawa ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bisa abin da ya kamata ya zama tushen auren wanda shi ne sadaki.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Lauyan tsohon mijin Umar I. Umar ya ce za su yi nazari kan hukuncin kuma za su jira mataki na gaba daga wanda yake karewa kan ko za su kai ga kotun daukaka kara a kan lamarin ko a’a.

Ya ce sun yi iya kokarinsu wajen daidaita dangantakar da ke tsakaninsu musamman yadda ta haifa masa ‘ya’ya hudu amma ba a samu sakamakon da ake so ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *