Kotu ta Tsare Mutum 29 da Ake Zargi da Fafutukar Kafa kasar yarabawa

Screenshot 20240418 134706 Facebook

Kotun majistre ta Iyaganku da ke Ibadan ta bayar da umarnin a tsare mutum 29 da ake zargin masu fafutukar kafa ƙasar Yarabawa ne saboda yadda suka yi wa harabar sakatariyar jihar Oyo ƙawanya.

Alfijir Labarai ta ruwaito a ranar Laraba ne aka gurfanar da mutanen saboda zargin su da hannu a harim da suka kai kan sakatariyar da kuma ofishin gwamna da bai yi nasara ba.

A baya-bayan nan ne wasu mutane da suka rufe fuskarsu suka yi dirar mikiya a sakatariyar jihar inda suka kafa tutarsu kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.

A cewar jaridar Vanguard, mutanen waɗanda ke fuskantar tuhume-tuhume bakwai kan haɗa baki da cin amanar ƙasa da kuma shiga haramtacciyar ƙungiya da riƙe makami cikin jama’a da kuma aikata abin da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba.

Mutanen da ake zargi, har da wata matashiya da manyan mata biyar, an tsare su a gidan gyaran hali da ke Ibadan bisa umarnin babban majistare, Olabisi Ogunkanmi.

Daga bisani kuma mai shari’ar ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 1 ga watan Agusta.

RN

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *