Kotun Ƙolin Najeriya ta haramta wa gwamnonin jihohin ƙasar rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.
Alfijir labarai ta ruwaito a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis kotun ta ce rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.
Ministan shari’ar ƙasar ne ya shigar da ƙara a gaban kotun a madadin gwamnatin tarayya, inda ya buƙaci kotun ta hana gwamnonin jihohin rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙanann hukumomin.
Tun da farko, gwamnonin jihohin ƙasar 36, sun nuna adawa da ƙarar da gwamnatin tarayyar ta shigar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj