Kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Nafiu Bala ya shigar kan zaben Muhammad Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar Gombe.
Alfijir labarai ta rawaito Kwamitin alƙalan mai mutum biyar na kotun kolin karkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta yi watsi da karar jim kadan bayan masu daukaka karar sun janye karar.
A halin da ake ciki, kotun kolin ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar Juma’a domin yanke hukunci kan sauran karar da Jibrin Barde na jam’iyyar PDP ya shigar.
Kwamitin ya sanya ranar Juma’a ne domin yanke hukunci jim kadan bayan da bangarorin suka amince da kuma gabatar da jawaban da suka yi a cikin karar, wanda zai kare ranar Lahadi 21 ga watan Janairu.
Kotun kolin ta fadawa lauyan ADC da lauyan Bala, Herbert Nwoye, cewa sun kasa kare wadanda suke tsayawa don haka sun kori karar, don gudun batawa kotun lokaci.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V