Kotun daukaka kara ta tabbatar da korar Aminu Chindo, ta tare da umurta INEC ta ba Sani Dallami na jam’iyyar APC shedar lashe zaben dan majalisar wakilai ta mazabar birnin Katsina
Alfijir Labarai ta rawaito Kotun dake zamanta a Abuja ranar Laraba, ta tabbatar da hukuncin kotun korafe-korafen zabe dake Katsina, wadda ta kori dan majalisar wakilai na mazabar cikin birnin Katsina Hon Aminu Chindo na jam’iyyar PDP.
A zaman kotun na kotun daukaka kara, wadda ita ce kotun karshe dake sauraron kararrakin zaben yan majalisun dokoki, ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ba Hon Sani Dallami satifiket din lashe zabe, ta kuma umurci wanda ake karar da ya bayar da tarar Naira miliyan ɗaya ga Sani Dallami bisa bata masa lokaci da ya yi
Kotun ta ƙwace kujerar Hon. Aminu Chindo ne, sakamakon laifin amfani da takardun bogi wanda kotu ta same shi dasu, wajen shigar da bayanan takara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ